Dandalin Yanar Gizo na Gwamnatin Amurka a hukumance

TOR ayyuka mafiya dacewa

Akwai hanyoyi da dama da za ku iya inganta tsaro don kanku yayin da kuke amfani da manhajar shiga intanet cikin sirri taTOR. Baya ga amfani da TOR, muna ba da shawarar amfani da ingantaccen layin intanet mai tsaro wato Virtual Private Network (VPN) don inganta tsaron ga ayyukanku a intanet. Idan mutum ya fara amfani da wani layin intanet a wajen ƙasarsa kafin fara amfani da TOR, za a tsare sawunsa daga masu bin diddigi. Akwai kayan haɗi masu yawa da muke ba da shawarar a yi amfani da su a cikin manhajar shiga intanet ta TOR a ɓangaren :safety and security”da ke cikin TOR. Da farko, kunna VPN ɗinku. Sannan:

  1. Buɗe manhajar TOR
  2. Je ku sashen saiti na TOR ku zaɓi “Privacy and Security”
  3. Cika akwatin “Delete cookies and site data when TOR browser is closed”
  4. Sauƙa ƙasa zuwa sashen History: Sauya saitin zuwa “Never remember history”
  5. Sauko zuwa Permision: latsa saiti don neman sauya kyamara “Daƙile sabuwar buƙata ta neman samun damar amfani da kyamararka”. Aikata hakan ga makirfo Don samun ƙarin tsaro, rufe kyamarar na’urarku ta gaba da salatif ko wani abu.
  6. Sauko zuwa security: latsa “Safest” Hakan zai dakatar wasu ayyuka a cikin TOR amma zai samar da layi mafi tsaro.
  7. Sauko zuwa HTTPS-Only Mode: Latsa Enable HTTPS-Only a dukkan windows. Wannan zai tabbatar da duk layukanku sun samu katanga da kuma tsaro.
  8. Ku je cikin saitin “TOR” ƙarƙashin “Privacy and Security”
  9. Cike akwatin “Use a bridge”
  10. Latsa “Request a bridge from torproject.org”
  11. Saka rubutun da kuka gani
  12. Yi amfani da adireshin https://coveryourtracks.eff.org da https://ipleak.net don ganin waɗanne bayanai ne za su rage da za su iya sakawa a bi sawunku a intanet.

Hanyoyi mafiya tsaro da za ku yi aiki da TOR da kuma layin ba da rahoto na Lada Don Adalci na TOR:

  1. Yi amfani da amintaccen layin VPN da kuka saya da kuɗi da kanku. Layukan VPN na kyauta ba kodayushe ne suke da tsaro ba.
  2. Haɗa na’urarku da amintaccen layin VPN sannan ku zaɓi wuri wajen ƙasar da kuke amfani da TOR a lokacin.
  3. Buɗe manhajar TOR
  4. Tsara saitin tsaro na TOR yadda kuke so.
  5. Don samun ƙarin tsaro, yi amfani da proxy na fili kamar na shagon shan shayi ko kuma na otel ta yadda ba za a iya gane takamaiman adireshin gidan da kuke ba.

Adireshi-adireshi na bayanan tsaro a TOR:

  1. Bayaanai kan TOR Bridges: https://tb-manual.torproject.org/bridges/.
  2. Bayanai kan tsaro a TOR: https://tb-manual.torproject.org/security-settings/.

SUBMIT A TIP

Do Your Part. Secure a Safer World.

There are many ways to submit information to Rewards for Justice.

You may choose from multiple platforms and contact us in numerous languages. To process your information efficiently, we ask you to state your information as succinctly as possible, provide your name, location, and preferred language, and upload all relevant files such as photographs, videos, and documents to support your information. An RFJ representative will soon contact you. Please be patient, as RFJ reads every tip we receive.

Please open your Line app to submit a tip. The number is +1 202 702 7843

Please open your Viber app to submit a tip. The number is +1 202 702 7843

Please visit our Tor-based tips-reporting channel at: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Turo da Bayani

Ba da gudummawarku Samar da Duniya Mai Kwanciyar Hankali.

Akwai hanyoyi da yawa da za ku iya turo da bayani.

Za ku iya zaɓa daga wurare daban-daban kuma tuntuɓe mu a harsuna daban-daban. Don yin aiki da bayananku yadda ya kamata, muna buƙatarku da ku zayyana bayananku ƙarara, ku saka sunanku, da wurin da kuke, da harshen da kuka fi so, sannan ku ɗora dukkan takardun da suka dace, kamar ƙaramin hoto, da bidiyo da za su ƙarfafi bayanan naku. Jami’in shirin RFJ zai tuntuɓe ku nan gaba kaɗan. Muna roƙo da ku ƙara haƙuri saboda muna karanta dukkan bayanan da muka samu.

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Signal don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Line don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Telegram don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Viber don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Ku duba shafin da zai ba ku ƙarin bayani game da turo rahoto a: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Skip to content